16 Yuli 2025 - 22:55
Source: ABNA24
Jagora: Masu Laifi Kada Su Kubuta Daga Hukuncin Ubangiji

Jagoran juyin juya halin Musulunci: Masu laifi kada su kubuta daga azabar Ubangiji a matsayin wani bangare na nasarar al'ummar Iran

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa Allah madaukakin sarki ya ba da tabbacin samun nasara ga al'ummar Iran karkashin tsarin Musulunci da kuma karkashin tutar kur'ani da Musulunci.

Kamfanin dillancin labaran Ahlulbayt na kasa da kasa (ABNA) ya bayar da rahoton cewa: Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana hakan a safiyar yau a lokacin da yake ganawa da shugabanni da jami'an shari'a a Husainiyar Imam Khumaini (RA) yana mai cewa: "Tabbas kowa ya sani cewa Allah madaukakin sarki ya ba da tabbacin samun nasara ga al'ummar Iran karkashin tsarin Musulunci da karkashin tutar kur'ani da Musulunci, kuma tabbas al'ummar Iran za su yi nasara."

Manyan batutuwan jawabin nasa sune kamar haka;

- Yana da matukar muhimmanci bangaren shari'a su bibiyi wadannan laifuffuka na baya-bayan nan a kotunan shari'a - na cikin gida da na kasashen waje – wadannan al’amura suna da matukar muhimmanci da suka zama dole. Ya kamata mu yi hakan a lokuta da yawa a baya, amma mun yi sakaci tsawon shekaru. A wannan karon, bai kamata mu yi sakaci ba. Ko da bibiyar wannan batu da shiga kotunan kasa da kasa da na kare hakkin bil'adama, da kotunan cikin gida, zai dauki shekaru ashirin, to ba damuwa da hakan. Dole ne a ci gaba da wannan aiki, kuma a kama maduddugar masu laifi.

- Mutum na iya zargin kotun kasa da kasa da yin biyayya ga wani iko, kuma wannan zargi na iya zama gaskiya, saboda yana iya kasancewa mai biyayya ce ga wannan iko. To, wata rana yana iya zama haka, amma wata rana ba zai iya zama haka ba ne; alkali mai zaman kansa zai iya bayyana a wannan kotun da zai yi hukunci na gaskiya. Wannan shi ne batu na farko: Wajibi ne a dauki wannan lamari da muhimmanci, sannan a magance shi da karfi da kuma taka tsantsan, tare da la'akari da dukkan bangarori, insha Allah.

- Al'ummar Iran sun gudanar da gagarumin aiki a wannan yakin da aka yi a baya-bayan nan; wannan babban aikin ba aikin soja ba ne, sai dai na nuna azama da manufa da yarda da kai. Ace kaga wata al'umma, kasa, da rundunar soji da ke cikin wata kasa su sami wannan karfin gwiwa a cikinta, kuma su kasance cikin shiri don tunkarar ikon Amurka da karnukanta masu biyayya a yankin - yahudawan sahyoniya - gaba da gaba, wannan Jarumta da yarda da kai na da matukar kima da muhimmanci.

- Al'umma ta kai wani mataki na karfi inda ta tsaya tsayin daka wajen fuskantar wannan iko, ba tare da tsoronta ba, sai dai ta tsoratar da ita, da aiwatar da duk wani aiki da za ta iya. Wannan shi ne batu na biyu: ayyuka. Batu na farko shi ne Ruhiyya da tsayin daka kyam.

- Abin da nake cewa ya kamata kowa ya sani: masoyanmu da makiyanmu, da al'ummar Iran - su sun sani - shi ne cewa al'ummar Iran ba za su zama masu rauni a kowane fage ba. Domin muna da duk kayan aikin da ake bukata: muna da dabaru kuma muna da iko. Ko a fagen diflomasiyya ko na soja, za mu shiga duk wata arangama, da taimakon Allah, da karfi da shiri.

- Hare-haren makiya sun nuna cewa da yawa daga cikin lissafin da wasu ke yi a fagen siyasa da sauran fagage ba daidai ba ne. Siffar makiya ta fito fili, kuma da yawa daga cikin boyayyun manufofinsu, wadanda suka boye a cikin maganganunsu, sun bayyana a fili. Sun shafe watanni takwas ko tara suna shirin gudanar da aikin soji, yayin da wasu ke tunanin babu abin da zai faru. Duk da hakan amma mutane sun gane cewa gaskiyar ta bah aka batun ya ke ba.

– Allah Ta’ala ya wargaza shirinsu. Shi ne ya rusa wannan shiri, ya kuma shigo da jama’a cikin fage domin goyon bayan gwamnati da tsarin. Jama'a sun fito kan tituna, amma suna masu kishiyantar abin da makiya suka shirya.

- Kun ga kanku a talabijin maganganun mutane daban-daban, masu fuskoki daban-daban, kamanni, da tufafi. Ba wanda zai yi tunanin za su yi magana da irin wannan halin sadaukarwa. Eh, magana ta bambanta da yin aiki, amma aikin magana, da kuzarin da ke motsa mutum ya yi magana, yana da mahimmanci. Babu wanda ya yi tsammanin hakan, amma a zahiri ya faru. Wadannan mutane, duk da bambancin siyasar da suke da shi, wani lokacin ma har da sabani, kuma duk da tsananin rarrabuwar kawuna a mahangar addininsu, duk sun tsaya kafada da kafada da kafada da wannan babban hadin kai, wato wannan gagarumin kawance na kasa.

- Abin da nake so in ce shi ne: A kiyaye wannan yanayin. Kowa ya kiyaye shi, kowa a matsayinsa da nauyin da ya hau kansa: dan jarida ta hanyarsa, alkali ta hanyarsa, jami'in gwamnati a hanyarsa, malami a hanyarsa, limamin Juma'a a hanyarsa. Kowane mutum yana da alhakin wannan yanayin kuma dole ne ya kiyaye shi. Wannan ba ya cin karo da bambance-bambancen ra’ayin siyasa, haka nan kuma ba ya cin karo da rarrabuwar kawuna a bangaren addini. Tsayuwa kafada da kafada a cikin wannan yanayi na kare gaskiya ne kawai, da kare kasa, da kare tsarin mulki, da kuma kare kasar Iran madaukakiya.

Your Comment

You are replying to: .
captcha